Akwai Yiwuwar za’a Fuskanci Tsananin Zafi A Sassan Najeriya – NIMET

0

Hukumar Kula da Yanayi ta kasa NiMet ta Ankarar da yuwuwar fuskantar karuwar yanayin zafi a wasu birane na Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar, Muntari Ibrahim shine, ya bayyana a Abuja, zafin na iya karuwa zuwa ma’aunin yanayi 40 a garuruwan da al’amarin ya shafa cikin sa’o’i 48.

Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara.

Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma Borno.

Nimet ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun haɗa da wasu sassan Sokoto da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa.

NiMet ta yi gargaɗin cewa jihohi kamar a Bauchi da Gombe da kuma Adamawa na cikin haɗarin rashin jin daɗi musamman a ɓangaren lafiyarsu.

Hukumar ta sharwarci mutane da ke zaune a jihohin da abin zai shafa, da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here