Wata dattijuwa yar Najeriya na cikin yanayi na farin ciki yayin da Allah ya albarkaceta da samun haihuwar yan uku.
Bayan isowar kyawawan yaran duniya, matar mai suna funmiedeni ta garzaya dandalin TikTok don nuna yadda ta yi goyon cikinta a cikin bidiyo.
A cikin bidiyon mai tsawon minti 1 da sakan 20, matar ta taka rawar farin ciki yayin da take baje kolin tulun cikinta a kaya daban-daban.
Baya ga hoton tulun cikinta, matar ta kuma nuna hotunan kyawawan yaranta yan uku.
A cewar matan, wannan shine haihuwanta na fari tana da shekaru 54. Hakan ya bai wa mutane da dama mamaki cewa ta dauki ciki a irin wannan shekarun.