littafin shehin malami bakatsine da ya yi Shekara 120 a laburaren Jami’ar Amurka.

0

Laburare dakin adana littafai ne wanda mutane daban-daban ke zuwa domin karantu. Yawancin irin wadannan dakunan karatun na ajiye da littattafai ne na tsawon shekaru, musamman a manyan makarantu da kuma

jamio’i.

Littafin da za iya cewa shi ne mafi dadewa a dakin karatu kuma babu wanda ya are shi domin ya karanta shi ne wanda aka gano a dakin Karatu na Jamiar Yale da ke Kasar Amurka. Kunma littafin na wani Shehin Malami ne dan asalin Jahar Katsina.

Littafin na Larabci ne, da ya kai shekara dai-dai har 120 a dakin karatu na jamiar, da babu wanda ya bukaci a ba shi da sunan aro, wanda watakila ya tafi da shi gida na ‘yan kwanaki domin nazari ko kuma ya zauna
a wurin ya karanta.

Wannan littafin kuwa wallafar wani Shehin Malamin ne mai suna Muhammad Alkashinawi wanda ya rayu a shekarun 1700, wato cikin Karni na 18. Kuma wanda ya gano wannan littafi a dakin karatu na jami’ar har ya are shi domin nazari, ya kuma shiga tarihi a kan hakan shi ne Uztaz Umar Dahiru Bauchi, wanda yake karatun digirinsa na uku a Jami’ar Kolumbiya ta Amurka.

Muhammad Alkashinawi dan asalin Katsina ne, kuma duk da cewa bakar fata ne daga kasar Hausa, Shehun Malamin ya kware a harshen Larabci da fannin ilimin Mandaki da na Lissafi da kuma na Shari’ar Musulunci.

Malamin ya yi suna a harkar ilimi a yankin Afirka ta Yamma a waccan lokaci. Sai kuma ya koma kasashen Larabawa na Hijaz a inda a nan ma ya yi ficen da har yake bayar da karatu, ga Larabawa a Haramin Makka. Shehin Malamin ya rasu a kasar Masar inda aka binne shi a makabartar da ake binne mashahuran malamai.

Jamiar Yale tana daya daga cikin mashahurai kuma dadaddun jamio’ia duniya, shi kuma Umar Dahiru daya daga cikin ya’yan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne, kuma cikin aikinsa na karatun digiri ne ya gabatar da makala mai taken “Binciken Hanyoyin Karatu da Yada Ilimi a Karni na 18: Ayyukan Alkashinawi (ya rasu 1742) na Ilimi a Yankunan Hijaz da Kasashen Bakar Fata” Ya kuma gabatar da makalar tasa cea karkashin Makarantar Nazarin Harkokin Addini a taron karawa juna sani kan yadda karatun soro da muka gada a yankin Afirka ta Yamma ya ba da gudunmawa wajen yada ilimi a yankin.

Mun Ciro Daga Jaridar Aminiya

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here