BINCIKE NA MUSAMMAN: MULKIN KAMA KARYA A KARAMAR HUKUMAR KURFI

0

Daga Wakilanmu @Katsina City News

Wani bincike da jaridar Katsina City News ta gudanar, ta gano a dukkanin shugabannin kananan hukumomin da aka zaba a shekarar 2022, Karamar Hukumar Kurfi na daya daga cikin inda ake mulkin-mulaka’u, tare da take duk wata doka da aka shimfida ta tafiyar da mulki.

Wakilan jaridun Katsina City News, sun ziyarci Karamar Hukumar Kurfi a ranakun Talata 3 da kuma Laraba 4 watan Mayu, domin jin ta bakin mutanen Karamar Hukumar a kan irin mulki da zababben Shugaban Karamar Hukumar yake gudanarwa, Alhaji Mannir Shehu wurma.

 

Ra’ayoyin da jaridun suka tattaro wadansu har da amincewa a dau hoton bidiyonsu kare bai ci. Al’mmar garin sun bayyana Shugaban Karamar Hukumar yana daukar kansa da tafiyar da mulki kamar wani Sarkin sarakuna mai daraja ta daya da wukar yanka.

 

Ba abin duk wata doka a tafiyar da aikin Karamar Hukumar, mun samu cikakken bayanin yadda ya dakatar da mataimakinsa ba tare da bin kowacce ka’ida da doka ta gindaya ba.

 

Takardar da muka gani ita ce, a ranar 17 ga watan Afrilu aka rubuta wa VC Nazifi Rabe aka ce an dakatar da shi. A ranar 3 ga watan Mayu, Shugaban Karamar Hukumar ya rantsar da sabon mataimakinsa, wanda ya nada ba tare da bin duk wata ka’ida ba.

 

A ranar 4 ga watan Mayu aka aika wa da halastaccen mataimakin Shugaban Karamar Hukumar da takardar tsigewa. Kamar yadda dokar kananan hukumomi ta nuna yadda aka tsige Shugaban Karamar da nada wani, hakan da aka yi ya saba wa ka’idar da aka gindaya guda 11.

 

A dokar da take rubuce, kuma kundin yake hannun kowanne Shugaban Karamar Hukuma, ana iya daukar wata uku zuwa hudu ba a kammala ka’idar cire mataimakin Shugaban Karamar Hukuma ba, amma a Karamar Hukumar Kurfi cikin kwanaki aka kammala komai.

 

Jaridun Katsina City News sun ga yadda Shugaban Karamar Hukumar ya kori nadadden Kansila mai kula da sashen ayyuka, Mani Ado Kurfi, shi ma ba tare da bin ka’idar da ta dace ba.

 

Takarda da aka buga aka aika wa kafofin watsa labarai cewa an kore shi bisa zargin da ba a kira shi ya kare kansa ba.

 

Mai Unguwa Dayyabu Lankasta da shi da Hakimin Kurfi da Mai Garin Kurfi a wayar hannu suka ga takarda na yawo cewa an kore shi daga aikinsa na Mai Unguwa.

See also  An kori kansila mai kula da sashen ayyuka na karamar hukumar Kurfi daga kan mukaminsa.

 

Irin wadannan kore-koren sun zama ruwan dare. Wasu da ke jam’iyyun adawa sun yi zargi ana kai masu harin don cutar da su kai tsaye daga Ciyaman din. Misali kanin Alhaji Shu’aibu Iliya, wanda ake kira da Shagali, wanda ya jigo a jam’iyyar APC daga baya ya canza sheka zuwa jam’iyyar NNPP. Ya yi takakarar dan Majalisar Jiha har aka je zabe zagaye na biyu.

 

Daga zaben su zuwa yanzu, Karamar Hukumar Kurfi ta samu kudi daga gwamnatin Jiha sun kai Naira miliyan 160, amma duk fadin Karamar Hukumar babu aikin Naira miliyan 15 a tsaye.

 

Tun da aka zabe su, Shugaban bai taba kiran taron yadda za a sarrafa kudin da ake amsowa daga gwamnatin Jiha ba. Takardun da kuma samu na amsar kudin kananan hukumomi daga gwamantin Jihar Katsina sun tabbatar Kurfi ta amshi kudade masu yawa, amma me aka yi da su?

 

Aikin hanyar Wurma bincikenmu ya gano aiki ne na kai tsaye. Hayar motocin aka dauko daga Karamar Hukumar Dan Musa ana biyan Direba da kudin mai. Ana zargin ana iya fitar da wasu kudaden Karamar Hukumar da sunan aikin.

 

Ya ake da kudaden harajin da Karamar Hukumar ke samu? Ina kudin da gireda da rola na Karamar Hukumar Kurfi da aka kai kasar Nijar a Jihar Maradi? Domin su samo kudi? Amsar da jaridun Katsina City News suka kasa samu ke nan. Mun yi kokarin magana da Shugaban Karamar Hukumar abin ya ci tura.

 

A ranar da aka rantsar da haramtaccen mataimakin Wakilanmu na wajen, amma ba su samu magana da shi ba, sun koma ranar 4 ga watan Mayu sun nemi magana da shi, shi ma abin ya ci tura.

 

Babban Editan jaridun Katsina City News ya kira shi a waya sau hudu, yana yanke ta. Daga baya ya aiko masa da sakon zai kira shi. Kiran da bai masa ba har zuwa rubuta wannan rahoton. @Katsina City News. www.katsinacitynews.com. Jaridar Taskar Labarai. www.jaridartaskarlabarai.com. The Links News. www.thelinksnews.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here