Hajj 2023: Katsina za ta fara jigilar maniyyata a ranar 29 ga Mayu

0

Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Kuki, a ranar Talata, ya bayyana cewa hukumar za ta fara jigilar maniyyatan jihar a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Jaridar Punch ta ruwaito babban daraktan ya bayyana hakan ne a Katsina yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na aikin Hajji na 2023 da aka gudanar a dakin taro na hukumar.

Kuki ya ce hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da aikin Hajjin bana na 2023 a cikin nasara.

Ya yabawa masu ruwa da tsaki bisa goyon baya da sadaukarwar da suka ba su wajen gudanar da aikin Hajjin bara.

Babban Daraktan ya yi magana sosai kan shirin hukumar na fara jigilar jiragen kamar yadda aka tsara.

An kuma shaida cewa rukunin farko na maniyyatan jihar Nasarawa za su tashi daga Najeriya zuwa kasar Saudiyya a ranar 25 ga watan Mayun 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here