ƁARAYIN DAJI SUN SACE MANOMA MASU YAWA A YANKIN BATSARI

0

Misbahu Ahmad

@ katsina city news

Da sanyin safiyar yau talata 25-07-2023, wasu gungun ƴan bindiga dake kan babura ɗauke da miyagun makamai suka kai hare-haren taaddanci a gonakan mutanen Nahuta, Madogara da Zamfarawa dake cikin yankin Ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Maharan da wani ganau ya shaida ma jaridun mu,sun kai kimanin ɗari kowannen su ɗauke da bindigogi kala kala , sun rutsa da mutane gonakansu, inda suka afka ma duk wanda suka taras yana aiki a gona, wasu sun sha dukan tsiya, wasu kuma sun tsira da harbi a jikin su. Maharan sun kwashi manoma masu yawa ciki hadda wani limami da mata da ƙananan yara.kamar yadda wani da ya sha da kyar ya tabbatar ma wakilanmu.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana mana cewa, ranar litinin 24 ga watan yuli da yamma ƴan bindiga sun ɗauki mutane ukku da suka je gona aiki, ya ƙara da cewa abun ya zama ruwan dare ta yadda komai kusancin gonar ka da gari ba lalle bane kaje aiki ka tashi lafiya. Sai in Allah ya tsallakar da kai domin a faɗar shi maharan suna bi gona-gona suna farautar mutane tamkar yadda kyanwa ke farautar naman dai.

See also  Sarkin Katsina Ya Bukaci A Goya Ma Sabon Makaman Katsina Baya.

Mai bamu labarin,ya bayyana cewa a kwanakin baya,in barayin sun kama mutane, a gona, sai su tafi da su, su tsare su da makamai suyi masu aiki iyakar zarafi, ga yunwa, ga ƙishi kuma idan mutum baiyi aiki mai kyau ba sai su lakkaɗa masa dukan tsiya.

Duk wani kokarin jin ta bakin yan sanda yaci tura, wakilanmu sun je ofishin kakakin yan sanda na jahar katsina amma baya ofis.

Katsina city news

@ Www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@ www.jaridartaskarlabarai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here