
Masu Bukata Ta Musamman A jahar Katsina Sun Bukaci Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda Data Sanya Su Acikin Mambobin Majalisar Zartarwa.
Hakan Nakunshe Acikin Wata Takardar Manema Labarai Data Fito daga Kunginyar (Katsina state APC Physically Challenged Stakeholders) Mai Dauke dasa Hannan Jami’in Hudda da Jama’a na Kungiyar Aminu Yahaya.
Takaradar ta Bayyana Masu Bukata Tamusamman Sunbada Gudunmuwa wajen Samun Nasarar Jami’iyar APC Tunda Ga Kafuwarta Zuwa Yau, Akwai Bukatar Samar masu da Mukamai Abangaren Majalisar Zartawa, Ko a wasu Bangarorin Gwamnati Domin Susan Ana Damawa Dasu.
Takardar Manema labaran Takuma Tunasar Cewa, Nuna Wariya Ga Masu Bukatar Tamusamman Amatsayin abunda Ya Saba Dokar Kundin Tsarin Mulkin na Jahar Katsina da Nijeriya Baki daya.
Takardar takuma Taya Gwamna Malam Dikko Umar Radda Murnar Cika kwanaki 100 akan mulki tare da Shan alwashin goyan bayansu Domin Sauke Nauyin daya Rataya Akansa na Al’ummar jahar Katsina.