Mutum 15 sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Adamawa

0

Aƙalla mutum 15 ne suka mutu bayan da wani kwale-kale ya kife a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da maraicen ranar Juma’a lokacin da kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji 23 ciki har da manoma da ‘yan kasuwa da ƙananan yara ya taso daga ƙauyen Rugange zuwa garin Yola a kogin Njuwa.

Rahotonni sun ambato wani jami’in ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross na cewa an tsamo gawarwaki hudu a wurin da lamarin ya faru, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Ya ce iska mai ƙarfi ce ta tilasta wa ruwa shiga cikin kwale-kwalen, wanda nan take ya kife da fasinjojin da ke cikinsa.

See also  EndSARS: Jihar Legas na nema Tiriliyan daya don sake gina wuraren da aka lalata mata

Ya yi kira hukumomin jihar da su samar wa al’ummar ƙauyen Rugange waɗanda ke fuskantar matsalar ambaliya duk shekara  jirjin ruwa mai amfani da inji.

Sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ADSEMA, Muhammad Amin Sulaiman, ya ce an kuɓutar da mutum bakwai yayin ake ci gaba da neman bakwai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here