Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai gana da shugabannin haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE) a yayin wani yada zangon da zai yi a birnin Abu Dhabi na UAE.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa za a. gudanar da ganawar ne domin warware matsalolin diflomasiyya da ke tsakanim ƙasashen biyu.
Matsalolin sun haɗa da hana biza da ƙasar ta sanya akan ƴan Najeriya tun watan Oktoban 2022 da dakatar da zirga-zirgar jiragen Emirates zuwa Najeriya.