‘Yan sanda a Kaduna sun kama gawurtaccen barawon akuya

0

Yan sanda a Kaduna sun kama gawurtaccen barawon akuy

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wani da ake zargin barawon akuya ne a kauyen Pasali Konu da ke karamar hukumar Kagarko.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), ASP Mansur Hassan, wanda ya yi magana da manema labarai a Kaduna ranar Lahadi, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar.

Hassan ya ce an kama wanda ake zargin mai shekaru 20 a ranar 11 ga watan Nuwamba da misalin karfe 04:30 na yamma a hannun ‘yan banga da jami’an sa ido da ke sintiri a unguwar.

Ya ce wanda ake zargin dan kauyen Igwa ne na karamar hukumar Kagarko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here