Ƴan Sanda Sun Kama Mutane 2 Bisa Zargin Fashi Da Makami a Katsina

0
ASP Abubakar Sadiq Aliyu
ASP Abubakar Sadiq Aliyu

Daga Muhammad Kabir, Katsina

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane biyu bisa zargin su da aikata fashi da makami a jihar.

Rundunar ta ce ta kama mutanen ne ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 2023,

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka a hedikwatar hukumar.

ASP Sadiq Aliyu yace rundunar tayi nasarar kama Saifullahi Zailani, ɗan shekara 22 da haihuwa da Abdulkadir Usman wanda akafi sani da Tahi dan kimanin shekara 18 da haihuwa, dukkan su suna zaune a unguwar Inwala a cikin birnin jihar Katsina.

“An kama su ne abisa laifin fashi da makami”

ASP Sadiq Aliyu ya kara da cewa “Rundunar ta samu wani bayani na sirri a ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 2023, cikin gaggawa jami’anmu suka isa wajen, inda suka cika hannunsu da waɗan da ake zargin.

See also  RIKICIN PDP A KATSINA SALISU ULI YA SHIGAR DA KARA.

“A yayin gudanar da bincike rundunar ta samu ƙaramar bindiga ƙirar turawa tare da harsashen ta guda shidda.”

“An samu waɗan da ake zargin da mota ƙirar Toyota 2023 ƙirar LE.”

Har ila yau rundunar na neman wasu da suke da sa hannun kamar haka, Muhammad, Abdul’aziz da Abdul. Ana neman su ruwa a jallo.

*************************************

Muhammad Kabir Katsina, ya shafe tsawon shekaru biyu yana kawo labaran Hausa a wannan gidan jarida na Taskar Labarai, a ɓangaren al’amuran yau da kullum, siyasa da labarukan ban mamaki da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here