Akalla gawarwakin mutane tara ne aka tsinto daga wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja a makon jiya.
Ku tuna cewa kimanin mutane goma yawancinsu ‘yan kasuwa ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a ranar Alhamis 16 ga watan Nuwamba.
Shugaban sashen bayar da agajin gaggawa na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, NSEMA, Alhaji Salihu Garba ya shaida wa NAN a ranar Lahadin da ta gabata cewa ya zuwa yanzu an gano gawarwakin tara daga cikin goman.