Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, ta gano wasu ma’ajiyar danyen man fetur ba bisa ka’ida ba, tare da cafke wasu mutane biyu a wani samame daban-daban da ta gudanar a fadin jihar Imo.
Hukumar NSCDC ta raba bayanan wadannan ayyuka a shafinta na Facebook ranar Lahadi, tare da hotunan da ke nuna nasarar aiwatar da ayyukan.