‘Yan Sanda A Jihar Kano Sun Gargadi Masu Shirin Yin Zanga-Zanga

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi kira ga al’umma  su kwantar da hankulansu, su kaucewa shiga duk wani nau’i na haramtaccen  taro, ko zanga-zanga, ko tattaki da ka iya haifar da tarzoma.

Rundunar, a cikin wata sanarwa da kakakinta, Haruna Kaiyawa, ya fitar, ta ce sahihin bayanai da ke hannunta, sun ce wasu kungiyoyin magoya bayan wata jam’iyyar siyasa na amfani da kafafen yada sada zumunta, suna tara jama’a da shirin fitowa kan  tituna domin nuna adawa da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan, Mohammed Usaini Gumel, ya yi kira ga daukacin al’ummar da su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani nau’i na taro, ko zanga-zanga, ko Tattaki.

See also  Duk wanda ya yi mana siyasar dabanci a Kano zai ɗanɗana kuɗar sa – Ganduje

Ya ce duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a Jihar za a kama shi kuma zai  fuskanci fushin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here