24 Ga Watan Satumba Ita ce Ranar Bin Ka’idojin Rubutu Ta Duniya.

0

 

24 Ga Watan Satumba Ita ce Ranar Bin Ka’idojin Rubutu Ta Duniya.

“Shakka babu bin ka’idojin rubutu ya na ceton Rayuwa”

Babu shakka bin ka’idojin rubutu abu ne mai matukar muhimmanci, domin alamar tambaya kadai na iya sauya ma’anar jimla, duk kuwa da irin kai-koma da ake da shi wajen yin amfani da su yadda ya dace.

A Hausa an fi samun matsala kan abin da ya shafi raba kalma da hada ta da kuma wasu alamomin tayar ko fitar da ma’ana.

Misali:

1. Sakamakon jarabawa ya fita?

2. Sakamakon jarabawa ya fita

3. Sakamakon jarabawa ya fi ta

Wadannan jimloli uku da ke sama za aga cewa duk haruffan da ke cikin su iri daya ne, amfani da alamomin rubutu ne kawai ya sauya su.

Kuma kowace jimla in aka yi amfani da ita in da ba mahallinta ba to sakonta zai iya sauya wa.

Hikimar da ke tattare da amfani da Ka’idojin rubutu abu ne da ya kamata duk wanda zai yi amfani da harshe ya sani, musamman ma ta fuskar rubutu.

See also  LABARIN MAI SOSA ZUCIYA DA SA HAWAN JINI GA YAN JAMIYYAR PDP MASU KAUNAR TA

Jeff Rubin shi ne wanda ya kirkiri ranar amfani da ka’idojin rubutu, kuma shi ya kirkiri shafin nan mai suna www.nationalpunctuationday.com.

Amfani da ka’idojin rubutu wata babbar gwagwarmaya ce ga mutane musamman wadanda suka jajirce wajen ganin cewa an yi amfani da ka’idojin a cikin rubutu, irin su ruwa biyu da aya da wakafi da alamar zancen wani da alamar motsin rai da sauransu.

Shin Ka’idojin rubutu suna da wani muhimmanci? Kwarai kuwa, domin ta hanyar bin ka’idojin rubutu ne kawai za mu iya inganta harshen mu, mu kai shi duk wani mataki na daukaka a duniya.

An kirkiri ranar Ka’idojin rubutu ne domin tunawa da darussan koyon rubutu da mu ka yi a makarantun Firamare da kuma karamar sakandire, domin mu dawo mu inganta rubutunmu da kuma bin ka’idojin harshenmu, da sanin abin da muke rubutawa.

A mafi yawan lokutta muna ganin cewa, ka’idojin rubutu kamar ba su da wata rawa da suke takawa, amma a zahiri su ne makasudin cigaban harshenmu da daukakarsa a duniya.

Domin karin bayani: https://www.daysoftheyear.com/days/2018/09/24

Daga Abdulrahman Aliyu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here