0

YANDA BARAYI SUKA MAMAYE WAGINI

Daga Lawal Iliyasu Garba

Damisalin karfe 11:30 pm na Daren yau asabar, wasu gungun barayin shanu dauke da manyan bindigogi suka mamaye garin Wagini dake cikin karamar hukumar Batsari a jahar Katsina.

Da shigar su cikin garin sai suka kama kiran Allahu Akbar hayyu alal jahad ina sojojin naku ina ‘yan bangar naku kamar yanda wani jiyau yake sanar da wakilinmu, daga nan sai su ka cigaba da kunnawa garin wuta musamman gidajen dake da kararuwa, gami da wani bangare na kasuwar garin, sun kashe mutum daya mai suna Sa’idu sun jima mutum ukku rauni, akwai Muntari akwai wata’yar uwa mai suna Binta matar malam Abubakar Wagini shahidi sun bugeta da gindin bindiga a hannu da kuma kirjinta, da kuma matar malam Muntari Gobirawa kanen malama Karima wacce ke da tsohon ciki yanzu haka tana asibiti tana karbar magani.

See also  YA SHAFE SHEKARA 15 YANA GYARAN HANYA

Bayan sun sa ma gidansu wuta, Yanzu haka dai sunyi awon gaba da shanu da tumaki masu yawa tare da kona motoci biyu da gidaje da dama.

Wannan hari da barayin su ka kai ana kyautata zaton na ramuwar gaiyane bayan ‘yan banga sun jera sati biyu suna kashe wadanda ake kyautata zaton barayi ne ciki harda Alhaji Bodori da Alhaji Ummaru Gwarko.

Lawal Iliyasu Garba
@ jaridar taskar labarai. Www.taskarlabarai.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here