NAJERIYA: Mai Karatun Digiri na biyu yana tura kurar Ruwa Dimin neman na Kai…

0

Hotunan wani dan Najeriya da ya kammala karatu yana tura ruwa a jihar Taraba ya bazu a kafar sadarwa ta Twitter.

Mutumin mai suna Kawu Malami ya karanci engineering Agricultural and Environmental Resources a Jami’ar Maiduguri.

Daya daga cikin takardun shaidar kammala karatun digirin digirgir a fannin Injiniya a UNIMAID data bayar a ranar 15 ga watan Junairu 2015 kuma tana dauke da sunan Kawu.

Har ila yau, akwai takardar shedar malantaka masu zaman kansu da cibiyar malamai ta kasa wadda take a Kaduna, data bashi a shekarar 2001.

Kawu ya kuma mallaki satifiket a fannin fasahar Aided Design da Jami’ar Maiduguri ta bayar a shekarar 2009.

Wani da yai tsokaci akai ya ce mutumin mai dakinsa ne yayin da wani kuma ya ce mutumin ya bar aikinsa a Bauchi ya tafi Taraba.

See also  CIBIYAR 'YAN JARIDA TA DUNIYA (IPI) RESHEN NIJERIYA TA ZABI SHUGABANNINTA

Legit.ng ta tuntubi Sulayman Abubakar wanda ya yi ikirarin cewa Kawu abokin zamansa ne a UNIMAID. Ya tabbatar da gaskiyar labarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here