A AKAYI MA IHU A KAROFI TA DUTSINMA WAJEN DAURIN AURE.?

0

WA AKAYI MA IHU A KAROFI TA DUTSINMA WAJEN DAURIN AURE.?
@ jaridar taskar labarai
A ranar asabar ne 9 /1/2021 ne akayi daurin auren wani jigon jam iyyar APC na karamar hukumar Dutsinma a garin karofi ta karamar hukumar Dutsinma jahar katsina
A daurin auren manyan daga ciki da wajen jahar sun hadu , jiga jigai a jam iyyar APC mai mulki a jaha da kuma tarayya.
Wani abu da ya dauke hankalin daurin auren shine Ihu da kuma sowa da kiran bama yi da akayi ma wani babba da ya halarci daurin auren daga katsina.
Wakilan mu da suke ta bin diddigin lamari tun asabar zuwa yau lahadi sun tabbatar da anyi wannan ihun.an kumayi a ture an kumace Bama yi .
Wasu masu ihun sun Kira jam iyyar PDP muke so, wasu kuma sun Kira da APC sai wane( inda suka Kira sunan wani da ake jin yana neman gwamna daga karamar hukumar kankia)
Wakilan mu sun kasa samun tabbacin ihun akan wa suke? Amma wasu na zargin da sakataren gwamnatin jahar katsina ake.dakta mustafa Muhammad inuwa Wanda ya halarci wajen daurin auren.
Binciken mu ya gano don gaban motarsa aka rikayi .kuma masu ihun sun rika bin motarsa da tana tafiya.
Masu ihun sun sake tare motar a wajen fita garin Dutsinma inda suka sake ihun nasu da jaddada basa yi .
Duk muryoyin da muka ji, wadanda aka dauka a waya, masu ihun basu kama sunan kowa ba.wadanda suke nuna dashi suke. Amma ganau sun ce masu ihun sun rika bin motar da sakataren gwamnatin katsina ke a ciki.sun kuma tare ta a wata hanya ta fita Dutsinma.
Dutsinma ta fara zama cibiyar nuna bijirewa da adawa tun kafin a buga kugen siyasar 2023.
Sati biyu da suka wuce sun yi ma arch Ahmad dangiwa ihu.wadanda yanzu ake ta binciken su waye.
Ko a zaben 2015 sai da aka kashe wani a garin karofi saboda yace sai PDP lokacin mutane na bukatar chanji zuwa APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here