Addini dabam siyasa dabam 

0

Addini dabam siyasa dabam

Inji Labaran Maku

Daga Zubairu Muhammad

 Tsohon Ministan yada labarai ta Qasa kuma xan takarar Gwamnan jihar nasarawa yayi kira ga alumman Nijeriya dasu kauracewa masu fakewa da siyasan addini. Labaran Maku yace’ wadannan mutanin sune masu cid a addini. Yac; babu wata jam’iyyar da take tin kaho da sunan addini kotace ita tana kare addini kaza ne. Musulunci ko Kiristanci ko addinin gargajiya.

Yace; duk Shugabannin da aka zavesu suna ratsuwa da Kur’ani ko baibul amma da zarar sun kama mulki sai ka rasa ina rantsuwar da sukayi sais u koma son raid a cin ammanar Talakawa da aka rantse za’a kula da rayuwarsu.

Yace; yau babu wanda zai ce Nijeriya akaw tsaro koda kuwa mutumin yana mulkine karyane yace an zaman lafiya a qasan nan . yace; talakawa suna fama da rashin tsaro garkuwa da mutani ya karene kan talakawa rikici yake- yake ya karene kan talakawa sune ake kashewa ake zubar da jininsu. Yace; manoma da makiyaya babu zaman lafiya Arewa ta tsakiya kullun kasha mutani akeyi Jihar Zamfara kullun kasha mutani akeyi Benuwe Nasarawa Taraba shin babu Shugabancine a qasa nan?. Ko kuma ba mutani bane ake kashewa ? shin ina Shugaban Buhari bai rantse cewa zai kare rayukan alumman qasan nan bane? Kokuma wadannan jihohin ba a Nijeriya suke bane?.

Labaran maku yace; an wayi gari yau Nijeriya qasarmu babu Jagorancin na kwarai Shugabanni basuyi koyi da magabata ba irinsu Sardaunar Sokoto Ahmadu Bello da Tafarawa Balewa Azzikiwe da sauransu, yanzu kowa abinda yaga dama shi yake aikatawa a mulkinsa babu ruwansu da matsalar Talakawa.

Labaran maku yace; Shugabanni su sani Allah zai tambayesu yadda suka tafiyar da malki kan Talakawansu. Su sani watarana basu bane a mulki, Maku ya roki alumman jihar Nasarawa dasu zave Jam’iyyar APGA saboda zata shere masu matsalarsu zata samar da zaman lafiya mai dorewa cikin jihar Nasarawa.

Yace; Manoma da makiyaya sai sunyi zaman lafiya sun koma suna aurataiya tsakaninsu. Sannan yadda Gwamnatin APC da Gwamna Al-makura suka talauta jihar Nasarawa suka sanya Ma’aikata day an fansho cikin damuwa idan Allah yasa ya zama Gwamnan jihar zai gyara matsalolinsu kowa zaiyi walwala. Yace; Gwamnatin Al-makura ta talauta jihar nasarawa ta sanya harkan kasuwanci ya tsaya cif Noma ya tsaya saboda rashin tsaro makiyaya suna fargaba. Harkan Ilumi ta tabarbare a Jihar Nasarawa

See also  Sarki Salman ya naɗa Yarima Bin- Salman a matsayin firaiministan Saudiyya

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan tabarbarewar Ilumi a Nijeriya

Daga Zubairu Muhammad

Majalisar Dinkin Duniya da hadin kwiwar wasu kungiyoyi sun koka akan tabarbarewar ilimi a Najeriya.

Sundai aika da sakon koken ne a ranar Malamai na Duniya, suka ce harkar ilimi shi ne ginshikin cigaban kowa ce Al’umma, ta yadda za ta iya rayuwa dan sanin hakin da ya hau kanta, ta yadda za su gane arzikin su kuma su amfana daga arziki din, kuma suyi mu’amala ta yadda ya dace a junar su.

Har ilayau kuma sai da ilimi ake iya kawar da fatara da talauci, kuma ilimi shi zai samar da al’umma ta gari.

Suka ce amma anan Najeriya harkar ilimi na can baya, saboda yawancin malaman da suke koyar da ilimin basu cancanta ba, dan haka za kuga koyarwar ba ta kai yadda ake so ba.

Majalisar Dinkin Duniyar da kungiyoyin, sun ce a binciken da suka gudanar a fadin Duniya sun gano cewa Yara sama da Miliyon 263 ne ba su samun damar zuwa makaranta, sannan kuma mayan mutane wadanda basu yi karatu ba a fadin Duniya sun kai kusan kashi 60.

Sun cigaba da bayyana cewa yake-yaken da ake yi a fadin Duniya yana kara kawo tsaiko wajen hana zuwan yara makarantu domin samun Ilimi.

Dan haka suna fatan ko wace kasa ta mai da hankali wajen inganta ilimin yara, saboda asamu damar kaiwa ga matsayar da aka aje akan harkar ilimi na 2030.

Taken taron dai na wannan shekaran shine, bada ingantace ilimi shi ne zai samar da malamai nagartattu. Kuma sun kawo wasu hanyoyi da suke ganin idan aka yi amfani dasu za su taimaka sosai a famnin ilimi.

Har’ila yau kuma sunja kunnin malamai akan su daina daukan darasin da basu da kwarewa akai, saboda hakan na kara kawo tabarbarewar ilimi, kuma sun ba da shawaran cewa ya zama wajibi a rinka ba Malaman makaranta horo daga lokaci zuwa lokaci, dan su kara kwarewa wajen harkar koyarwa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here