AIKIN GADA; ALLAH YA TSERATAR DA NI………Danjuma katsina
A yau Alhamis 3/2/2022 da misalin karfe 4:30 na yamma, Allah ya kiyaye da daya daga cikin motocin da ke aikin hanya sun markade ni da motata.
Ina tare da Yusufu Jargaba, Wakilin Rediyo Jamus, mun dawo gaisuwar mutuwar matar Sani Ahmad, Wakilin jaridar TELEGRAPH.
Bayan na ajiye Jargaba, sai na fada masa cewa, zan tafi filin kwallo in motsa jiki na.
Na baro ofis dina daidai gadar adeleke bangaren Hagu inda aka amince motoci su wuce. na iske motar aikin mai kaca tana kokarin juyawa, sai na tsaya aka ba wata mota hannu ta wuce. Ni ma zuwa can suka ba ni hannu in wuce, ashe shi kuma Direban motar mai kaca ya sanya ta juya ne, sai kawai na ji rumuts! Mota ta tankada ta kara gaba ta tsaya.saura kiris data hankada ramin gadar adeleke
Da yake gaban dimbin jama’a aka yi, kowa ya san ba ni da laifi. Direban mota mai kaca ya fito yana ba masu ba da hannu laifi, yana masu fada. Nan aka kewaye ni ana ban magana.
Hatta jajayen fatar da ke duba aikin da suka ji bahasin yadda abin ya faru, suka ce in bi su zuwa ofis.
Sun amshi mota ta da niyyar za su gyara mani. Yanzu haka tana wajensu.
Yadda suka nuna damuwarsu, ya dan sanyaya lamarin. Yanzu ina sauraronsu. Mota na wajensu. Sun ba ni hakuri. Sun kuma yi nadama.
A ofis dinsu wani ma’aikacin ya ce: “Kai Ogan jaridar Katsina City News ce. Ai kuwa suna ba mu hadin kai duk bidiyon ci gaban aikinmu su ke dora shi.”
Alhamdulillah na tsira. Allah kara tsare mu.ya Sanya mu wanye lafiya dasu.
@ katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com