Akan Bashin 850 Matashi a Kano ya cakawa wani Kaho a kirji

0

Akan Bashin 850 Matashi a Kano ya cakawa wani Kaho a kirji

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Rundunar’ yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai suna Dini Abdullahi dan shekara 20 da yunkurin kisa inda ya cakawa Ahmad D. Ahmad kaho a idonsa da kuma kirjinsa a unguwar Diso cikin birinin Kano,

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a ranar Talata, inda ya ce wanda ake zargin ya soke shi ne bayan da rigima ta kaure a tsakaninsu kan bashin 850,

Dini ya ce yana bin Ahmad bashin kudi N850 ne, inda shi kuma ya musanta, da hakan ta sanya suka fara rigima, har ya yi amfani da damar wajen raunata abokin fadan nasa

Ya kara da cewa tuni suka kama wanda ake zargin kuma ya tabbatar musu da cewa yana shan wiwi da kwayoyi.

See also  Bayan daura Aure an kawoma ita gidan ka da safe taje alwala kaga fuskar ta koma haka ya zakayi?

Ya kuma ce wanda ake zargin Dini Abdullahi ya amsa laifinsa, inda tuni kwamishinan ‘yan sanda ya bada umarnin a mayar dashi sashen binciken manyan laifuka na kisan kai domin a fadada bincike.

A nasa bangaren wanda ake zargi Dini Abdullahi ya ce ya caka masa kahon ne saboda yaki biyansa bashin da yake binsa.

“Dokin zuciya muka hau gaba dayanmu kuma da nasan haka za ta faru wallahi bazanyi mas ba,” a cewar sa.

Shi ma wanda aka raunata Ahmad D Ahmad ya ce a saninsa babu wani abu a tsakaninsu kawai dai ya tsinci kansa ne a gadon asibiti.

Sannan ya bukaci mahukunta da su bi masa hakinsa duba da yadda aka zalince shi ba tare da laifin komai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here