Allah ya tseratar da Dan majalisa

0

Allah ya tseratar da Dan majalisa
@ jaridar taskar labarai
Dan majalisar batsari da yan fashin daji sukayi ma kofar rago a garin garwa ta batsari ya samu tsira yanzu haka yana kan hanyarsa ta zuwa katsina a rakiyar jami an tsaro.
Wakilanmu sun jiyo cewa da Dan majalisar Alhaji jabiru yau yau yaje garin na garwa ne da yammacin yau domin ta aziyyar wata rasuwa da akayi.
Ana jin barayin sun san shigarsa shi ya Sanya suka kaima garin farmaki.
Da mutanen garin suka gane shine ake hari sun yi kokarin fitar dashi cikin garin ta wasu hanyoyin shiga da fita garin da suka sani fiye da barayin dajin.
Ta wadannan hanyoyin dan majalisar ya samu isa wani wurin da jami an tsaro suka kai masa dauki suka Taho dashi zuwa gari.
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here