An bude gasar karatun Alkur’ani ta jihar Kano

0

An bude gasar karatun Alkur’ani ta jihar Kano

Daga Ibrahim Hamisu, kano

A ranar Litinin da ta gabata ne aka kaddamar da fara gasar karatun alkur’ani a makaranta koyon harshen Larabci ta Kano da ake yiwa lakabi da S.A.S.

A jawabinsa a wajen bikin budewar shugaban hukumar kula da makarantun Al’qurani dana Islamiyyu na jihar Kano Gwani Yahuza Gwani Danzarga, ya bayyana cewa musabaqar ta bana zata bambanta da ta sauran shekaru saboda kawo sabbin tsare-tsare wanda za su yi dai-dai da zamani, inda ya kara da cewa an zakulo alkalai masu hazaka wanda za su yi alkalanci a bangaren maza da mata.

A na sa jawabin Kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sunusi Sa’id Kiru wanda ya samu wakilcin babbar sakatariya a ma’aikatar Hajiya Lauratu Diso, ta bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf domin ganin an gudanar da musabaqar cikin tsari, inda ta bayyana cewa tuni shirye-shirye suka yi nisa don tunkarar musabaqar ta kasa wadda jihar Kano zata karbi bakunci a farkon sabuwar shekarar 2021 mai kamawa.

See also  WATA SHARI A DA AKAYI A SHEKARAR 1950 A KATSINA

Manyan baki da suka halarci taron sun hada da manyan malamai musamman masu bayar da gudunmawa ta wajen musabaqa irin su Sheikh Ibrahim Shehu Mai Hula da Sheikh Yusuf Isyaka Rabi’u da Alkalin Alkalai na musabaqar bana Gwani Barrister Mukhtar Abdullahi Koki da kuma sauran mashahuran malaman jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here