AN DAGE FARA KARAR MAHADI SHEHU ZUWA WATAN 19 ga watan March

0

AN DAGE FARA KARAR MAHADI SHEHU ZUWA WATAN 19 ga watan March
muazu hassan
@ katsina city news
A yau 11/2/2021 babbar kotun tarayya dake katsina ta Sanya don fara sauraren karar da shugaban yan sanda na kasa ya shigar a madadin gwamnatin katsina akan sanannen mai kwarmaton nan a bisa yanar gizo mahadi shehu Dan asalin katsina mazaunin Kaduna.
Wakilan jaridun katsina city news sun halarci kotun don ganin fara shara ar da aka tsara zata fara a yau.
Amma da misalin karfe Goma na safe lauyoyin dake wakiltar yan sanda suka zo kotun kuma suka shiga wajen Alkaliyar
Bayan wasu mintuna suka fito suka tafi,daga baya muka samu bayanin cewa an daga zuwa 19 ga watan March don fara saurarar karar.
Dalilin da suka bayar shine har yanzu sun kasa samun mahadi shehu domin su damka masa sammacin da kotun ta bayar akan haka suka ce a kara basu lokaci.har sai sun samu mahadi shehu sun bashi sammacin.
Akan haka aka daga zuwa 19 na watan March 2021. A satin da ya wuce ne gwamnatin katsina ta shelanta kudurin kai mahadi kotu.a wani taron manema labarai da suka Kira.
Zaman farko za a karanta karar ne kafin a fara sauraren ta .in ba wata matsala a shigarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here