An Gudanar da Taron Wayar Da Kan Al’umma Akan Yadda Za’ayi Amfani Da Dokar Samar Da Bayanai Domin Samar Da Shugabanci Na Gari.

0

Taron Wanda Ya Gudana A dakin Taro Na Katsina Vocational Center A Yau 8/9/2022 Ya Samu Halattar Kungiyoyin Farar Hula, Yan Jarida Da Jami’an Gwamnati.

 

Shugaban Taron kwamaret Bashir Dauda Sabuwar Unguwa Ya Shaida Ma Jaridar Taskar Labarai Makasudin Taron.

 

Dauda Yace “Babu yadda Za’ai Dan Kasa ya Iya Bada Wata gudummuwa akan Abinda ya shafi tafiyar da Gwamnati kamar yadda dimukuradiyya ta tsara Idan Bai da Bayanai.

 

“Shiyasa mukaga ya kamata mu Yan gungiyoyin Farar Hula muzu muhadu Domin muyi kira ga Gwamnatin Jiha Akwai Doka wacce Akayita Ta Kasa ta Shekara 2011 Wadda Taba Yan Jarida Da Yan Kasa Yancin Samar Da Bayanai.

See also  CONSTRUCTION OF THE 50MW GAS-POWERED ELECTRICITY PLANT FOR BORNO STATE HAS GONE FAR!

 

“Dan Haka Mukaga Ya Kamata Dokarnan A Fara Aiwatar Da Ita.

 

Dauda Ya Kara Da Cewa “Akwai Jahohi Da Yawa Waɗanda Jahar Katsina Ma Tafisu Suna Cikin Tsarin Da Ake Kira Da OGP Amma Haryanzu Katsina Bata Shiga Cikin Tsarinba.

 

“Kuma Shiga Cikin Wannan Tsarin Yana Nuna Anayin Abun A Bude. Akwai Bukatar Katsina Tashiga Cikin Jahohi Ko Gwamnaroci Na Duniya Da Suka Sa Hannu Na Amincewa Zasubi Tsarin OGP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here