AN JANYE SOJOJIN MARA A DANMUSA

0

AN JANYE SOJOJIN MARA A DANMUSA
….Barayi har sun sace mata da yara
Muazu hassan
@ katsina city news
Sati biyu da suka wuce sojojin dake garin Marar zamfara ta karamar hukumar Dan Musa.suka kama wani barawon daji a kasuwa, suka kashe shi, suka yasar da gawar bakin gari.
Tun lokacin barayin sukayi ta yunkurin kawo Hari a garin amma da taimakon Allah, sojoji da kuma mutanen garin na mayar dasu.
Sati daya da suka wuce sojojin dake garin suka kwashe yana su yana su suka bar garin bayan sama da shekaru Goma suna kare yankin daga sansaninsu dake garin.
Daren alhamis da ta wuce,misalin karfe daya na dare, barayin suka shiga garin na Mara inda kai tsaye suka wuce gidan wani tsohon kansila mai suna Alhaji Idi Audu.
A gidan Alhaji Idi audu da karfi suka sare kofar gidan suka shiga, da karfin tsiya Suka tafi da matarsa mai suna, Sa’ adatu da goyon ta karamar yarinya mai suna fauziya da wani matashi mai suna Misbahu da yaro mai suna Musa.sun kuma tafi da wani matash mai suna Yusufu.
Barayin sun Kira Alhaji idi Audu inda suka Nemi a biya kudin fansa.kafin su sako iyalan da suka tafi dasu.
Garin Mara da sauran yankin dake kusa dasu suna a cikin firgici da tsoron me zai biyo bayan kwashe sojan da suka shafe shekaru sama da Goma a wajen suna taimaka masu.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here