AN KAFA KWAMITIN ZABEN SABBIN SHUGABANNI NA APC A JIHAR KATSINA.

0

AN KAFA KWAMITIN ZABEN SABBIN SHUGABANNI NA APC A JIHAR KATSINA.

Muazu Hassan
@Katsina City News

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Katsina sun yi taro a Kano jiya lahadi 4 ga watan Yuli, 2021 domin tattauna yadda za su fuskanci kongress na jihar daga matakin unguwani zuwa jiha.

A taron an rusa da lalata wani sunayen da wasu mutane biyu kacal suka yi ruwa da tsaki na fitarwa a matsayin sune masu ruwa da tsaki na kowace karamar hukuma a jam’iyyar APC ta jihar Katsina.

Tun kwanaki ake ta korafin wasu mutane biyu sun hadu a ofis din daya na gidan gwamnati sun fitar da wasu sunaye a matsayin dattawan jam’iyyar na kowace karamar hukuma.

Taron na jiya yayi fatali da wadanan sunayen ya kuma rusa duk wani shiri da wadannan biyun suka yi na tsarin yadda taron kongress zai kasance.

Taron ya sake sabon tsari inda aka nada Alhaji Muntari Lawal shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin Katsina ya zama shugaban taron Kongres na iahar Katsina.

See also  MATSALAR ZABEN DAN TAKARAR KARAMAR HUKUMAR SAFANA A APC

Sannan an tsara shugaban zai yi aiki da kwamitin wanda duk wani mai neman takarar gwamna a APC yana wakilci na mutum daya.

Sai sanatoci suna da wakilci, sai ‘yan majalisar tarayya suma suna da wakilci, sai ‘yan majalisar jiha.

Taron ya tsara babu ruwan shugabannin jam’iyya na riko na jiha da shiga harkar kongres wadannan kwamitin su ne zasu yi.

Daga tsara kongres na unguwani har zuwa na jiha har tafiya tarayya.

Majiyarmu tace kowa yayi farin ciki da taron na Kano da yadda aka tsara za a tafiyar da kongres din a jihar Katsina amma banda mutum daya da mutanen shi.

Katsina City News
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.081377777245
Email; katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here