AN KAI KAI HARI GARIN RUNKA
muazu Hassan
@ katsina city news
“Yan ta adda sun kai Hari garin Runka ta karamar hukumar safana a daren Lahadi da misalin karfe 11 zuwa 12 na dare.
Maharan Sun je gidan wani ma aikacin civil defens da yayi hijira zuwa katsina.
A gidan sun tafi da mutane uku wata tsohuwa da yarinya da kuma wani Namiji.
Yau litinin 1 ga watan Agusta.barayin sun harbi wata mota dake tafiyar wajen gari hanyar zuwa batsari.basu tafi da kowa a motar ba.saboda mutanen sun fashe.amma sun sace duk wani mai amfani a cikin Motar.
Runka tana a cikin karamar hukumar safana dake jahar katsina kuma tana kusa
da Dajin Rugu.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245