AN KAMA MACIJIN DA YA CIJI MAHADI SHEHU

0

AN KAMA MACIJIN DA YA CIJI MAHADI SHEHU
Muhammad Ahmad
@ jaridar taskar labarai
Rundunar yan sanda ta kasa dake hedkwatar yan sanda Abuja sun Sanya an Kamo macijin da ake zargin shine ya sari mahadi shehu Dan Rajin nan da gwamnatin jahar katsina ta kai korafi akan shi kuma suka gayyace shi domin amsa wasu tambayoyi
Majiyarmu ta tabbatar mana a yau Alhamis yan sandan suka gayyato wani mai kama macizai Wanda yazo da kayan aiki na magungunan gargajiya ya ba zasu.
Bayan ya kammala duk al adunsu da suke na kama maciji sai ya shiga nema.cikin lokacin kankane ya kamo macizai guda biyu.
Daya bakikkirin ne kato Wanda nan take aka kashe shi.dayan kuma ja ne siriri, mai kama macizan , yace a kyale masa shi da rai zai wani aiki dashi
Ana zargin bakikkirin shine Wanda ya sari Malam mahadi shehu. Koda yake Alhaji mahadi shehu ya karyata cewa wani maciji ya sare shi, ya karyata a kafofi da dama ciki harda hirar da wannan jaridar ta taskar labarai da tayi dashi.
Jaridar nan har yanzu bata samu wata takardar likita ba, da ta tabbatar maciji ya sari mahadi shehu, sai dai shaidun baka daga wasu yan sanda da jami ai asibitin kasa inda mahadi shehu ya kwanta na Dan wani lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here