AN KARA SACE WASU MUTANEN A BATSARI

0

AN KARA SACE WASU MUTANEN A BATSARI

 

Daga Taskar labarai

 

Wakilan Taskar labarai na musamman da zasu rika kawo mana abin da ke faruwa akan tsaro a yankin Batsarida Safana da Danmusa da kuma wani yanki na Jibiya ta jihar Katsina.

 

Sun ruwaito cewa a cikin ‘yan kwanakin nan an kara satar wasu mutane guda biyu daya wata tsohuwa ce mai suna Hafsat wadda aka sata a wani gari mai suna Madaddabai, wanda yake gabacin Batsari, wanda da suka sace ta sun yi magana da iyalanta suka ce sai an basu naira miliyan talatin kafin su sako ta.

 

Sun kuma sace wani mutum mai suna Isah a wani gari mai suna Salihawar Dantsuntsu, shi ma yana hannunsu.

 

A salihawar Dantsuntsu an so sace wani manomi amma da barayin suka dora shi bisa babur tsakiyarsu sai yayi dubara ya kada su ya kubce ya yi Daji da gudun tsiya.

 

Binciken Taskar labarai ya gano cewa an sako wasu da aka sace a yankin Kandawa su uku da kuma wasu da aka sace daga yankin Shekewa mutane biyu, Suma ana Jin an biya kudin fansa kafin a sako su.

See also  FG awards bridge contract to link Zango Kataf, Kaura LGAs across river Kaduna

 

Taskar labarai ta jiyo cewa wata mata ‘yar cikin Batsari mai suna Karima da suka sace ..sun ce akai masu miliyan daya, iyalan sun tara kudin da kyar da bashi sun kai amma barayin sun bugo suka ce wai basu suka amshi kudin ba don haka sai dai akai wadansu.

 

Taskar labarai ta jiyo cewa k Karima an kama ta ne a wata motar haya da wasu fasinjoji a cikin motar.

 

Wani Abu da Taskar labarai ta gano mafi yawan masu satar nan daga jihar Zamfara suke shigowa kuma a dajin da yayi iyaka da Katsina da Zamfara suke yin garkuwa da wadanda suka sata.

 

Duk wani kokarin jin ta bakin hukumar ‘yan sanda a kan lamarin yaci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here