An Kori Yan Gudun Hijira A garin funtua

0

An Kori Yan Gudun Hijira A garin funtua
@ jaridar taskar labarai

“Ku barmu a Funtua ko akan titi mu kwana” In ji yan gudun hijirar Faskari.

‘Yan gudun hijirar da ‘Yan bindiga suka tarwatsa daga kauyukan Karamar Hukumar Faskari wadanda suka shigo Funtua sun roki hukumomi da su bar su a Funtua kar su mayar da su Faskari saboda yanayin tsaro a Faskarin bai inganta ba.

Kwanaki biyar da suka gabata ne ‘yan gudun hijirar suka yi sansani a makarantar firamare ta Karofi da ke cikin garin Funtua mazansu da mata, tsofaffi da kanan yara.

Labari ya bazu a cikin garin na Funtua har al’umma sun fara kai masu tallafin kayan abinci da sutura kwatsam mahukuntà su ka zo su ka ce su bar makarantar su koma Faskari a cewarsu.

See also  Hikumar Hisbah ta jihar Kano za ta hana yin ‘fati’ da daddare

Wannan sanarwa ba tai masu dadi ba ganin yadda suka baro kauyukansu kuma suka baro garin na Faskari cikin fargaba da rashin tsaro da cunkoso a sansanin na Faskarin gashi kuma mata biyu daga cikin ‘yan Gudun hijirar sun haihu a sansanin daya ma tagwaye ta Haifa.

Yanzu haka dai ‘yan gudun hijirar sun fantsama cikin gari wasu a masallatai don neman masauki ganin cewa ga hadari gami da iska mai karfi ta taso ana sa ran ruwan sama a daidai lokacin da aka basu umurnin fita daga harabar makarantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here