AN NADA SHUGABAN ‘YAN BANGAR BATSARI DAKAREN RUMA.

0

AN NADA SHUGABAN ‘YAN BANGAR BATSARI DAKAREN RUMA.
Daga misbahu batsari
@ jaridar taskar labarai
Da safiyar juma’a 29-01-2021, Sarkin Ruman Katsina hakimin Batsari Alhaji Tukur Mu’azu Ruma, ya nada Isah Ibrahim Gyan-gyan sarautar Dakaren Ruma, nadin ya samu halartar ‘yan kungiyoyin ‘yan sintiri (vigilante) daga wurare da dama, kamar su Maryam Nasir wadda ita shugaban ‘yan banga bangaren mata na jihar Zamfara, sai shugaba na jihar Katsina baki daya Salisu Rabo Katsina, wanda yayi jawabin nuna jin dadin sa game da wannan matsayi da dan kungiyar su ya samu inda ya kara da cewa samun wannan sarauta yana da alaka da irin jajircewa da kwazo da suke nunawa wajen aiwatar da aikin su.
Haka kuma yayan wanda aka nada Malam Mansir shima yayi jawabi nuna farin cikin sa game da wannan sarauta da kanen sa ya samu ta Dakaren Ruma, daga bisani Isah gwangyan watau wanda aka nada sarautar yayi godiya ga Allah da ya bashi wannan sarauta, kuma yayi godiya ga Sarkin Ruman Katsina da ya bashi wannan sarauta ta Dakaren Ruma, daga nan sai yayi fatan alheri ga dukkan wadanda suka samu halartar taron, haka Kuma yayi fatan Allah ya maida kowa gidan sa lafiya.
Daga nan sai aka cigaba da shagulgulan murna inda aka gabatar da shugaban ‘yan bangar na Matazu mai suna Umar Kaura domin ya nuna irin tasa bajintar, wanda yana fitowa sai ya fiddo wani gwangwani ya zuba masa wani ruwa da garin magani sai ya kyarta ashana ya sai wuta ta kama cikin gwangwanin sannan ya dinga zaro wasu allurai daga cikin hancinsa kuma ya zaro wata sharbebiyar wuka yayi ta yankawa a wuyansa saida aka kwace, wani dake kusa dashi shima ya zaro wata wuka ya dinga babbala ta kamar ana balla sakaina, in takaice maka zance andai yi abubuwan ban mamaki da dama.
Haka kuma duk a ranar ta juma’a Sarkin Ruman Katsina ya nada Muntari Abdu sarautar Raya karkaran Ruma, kuma ya nada Kabirun Malam Sarkin wakar Sarkin Ruma.

See also  THE BUHARI ADMINISTRATION HAS DONE 10,053 WATER PROJECTS IN JUST 6 YEARS!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here