Rahotanni daga Birnin Gwari a jihar Kaduna na cewa ‘yan bindiga sun sace sama da mutum 80 a kan wata babbar hanya.
Wani Jami’an Kula da Motocin Haya ta NURTW, sun ce an sace mutanan ne a kan wata babbar hanya da ta hada arewaci da kudancin kasar.
Wasu Mazauna yankin da jami’an sufuri Birnin-Gwari sun ce a ranar Lahadi ne ‘yan bindiga suka tsayar da motoci da dama, suka sace dumbin matafiya tare da shigar da su cikin daji, suka kuma bar motocinsu a wajen.
Sai dai har yanzu jami’an ‘yan sanda ba su ce komai ba game da lamarin.