AN SAKE GABBATAR DA MAHADI SHEHU A KOTU

0

AN SAKE GABBATAR DA MAHADI SHEHU A KOTU
muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
A yau Talata 16/3/2021 hukumar yan sanda ta jahar katsina ta sake gabatar da mahadi shehu a kotun majistire dake katsina.
An zauna kotun, amma ba a karanta tuhumomin da ake ma Mahadi shehu ba , saboda lauyan mahadi shehu yayi korafi a rubuce ga kotun cewa Wanda yake karewa baya da lafiya ba zai iya zaman sauraren shara a ba.
Lauyan hukumar yan sanda yayi korafin cewa a takardar da lauyan mahadi ya rubuta babu wata hujjar daga asibiti ko likita.
Lauyan mahadi shehu yace duk da babu wannan amma ai ga Wanda yake karewa ana iya ganin shi kwance magashiyan .

See also  Buhari Ya Cire Wanda Ake Zargi Da Kunnowa Ganduje Wuta


Bayan muhawarar lauyoyin biyu . Alkalin ya daga daukar matsaya zuwa ranar Talata 30/3/2021.inda zai bayyana ko zai ci gaba da shara ar ko a a .
Akan haka aka mayar da mahadi shehu zuwa wajen yan sanda har sai ranar da za a dawo.
@ jaridar taskar labarai www.taskarlabarai.com
@ katsina city news www.katsinacitynews.com
@ the links news www.thelinksnews.com
07043777779
08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here