An Tube Rawanin Dan Sule Lamido Daga Sarautar Hakimi
Masarautar Dutse da ke jihar Jigawa ta tube rawanin dan Tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido, wanda ya ke matsayin Hakimin Bamaina, Mustapha, Lamido daga mukaminsa bisa zarginsa da hada harkar sarauta da siyasa.
A cewar masarautar za ta sanar da sabon Hakimin da zai maye gurbinsa a nan gaba.
Majalisar masarautar Dutse ce ta amince da tube wa Alhaji Mustapha Lamido rawaninsa na hakimcin Bamaina. An tube shi ne bayan masarautar ta fara dakatar da shi daga mukaminsa na Hakimin masauratar.
Wata sanarwar da ta fito daga majalisar Masarautar Dutsen, wadda Sakatarenta Ahmadu malami ya rattaba wa hannu ta zargi Alhaji Mustapha Lamido da shiga harkar siyasa dumu-dumu, alhali yana basaraken gargajiya.