Anyabawa Sojojin Nijeriya saboda ceto Qananan yara 183 a wajen Boko haram

0

Anyabawa Sojojin Nijeriya saboda ceto Qananan yara 183 a wajen Boko haram

Daga Zubairu Muhammad

Kungiyar NICEF ta nuna matukar jin dadinta da sakin kananan yara su 183 da Sojojin Najeriya suka yi a Barno.
Sojojin dai sun saki kananan yaran ne a ranar Alhamis din da tagabata. Kananan yaran wanda shekarun su ya kama daga 7 zuwa 18, an kamasu ne hade da mayakan Boko Haram. Cikin su kuma a kwai mata 8 sai kuma Maza 175.dake hannun mayakan.

Dayake jawabi a madadin Kungiyar UNICFF
Muhammad Fall ya nuna matukar murnan shi game da veto rayuwan Yaran, ya ce “za mu yi aiki tare da gwamnatin jihar Barno ta hannun ma’aikatan walwala da jin dadin mata da sauran Jama’a, dan samarwa yaran rayuwa ingantacciya”.

See also  YADDA BARAYIN SHANU SUKA KAI HARI RUMA

Muhammad Fall ya kara da cewa kuma ” mu na yabama Jami’an tsaro, da kuma Gwamnatin Jihar Barno game da wannan namujin kokari da suka yi, kuma hakan zai kawo karin zaman lafiya a cikin al’umma.

Kungiyar dai sun ce za su duba lafiyar yaran kafin su mika su ga iyayen su dan su je su fara sabuwar rayuwa kamar na sauran yara.
In ba’a manta ba dai kungiyar ta UNICEF tun a 2017, suke irin wannan aikin na inganta rayuwar yara wadanda ake kamasu a rikicin Boko Haram, wanda a yanzu haka sun inganta rayuwar yara 8,700, kuma suka hada su da iyayen su, a inda yanzu haka suna nan suna gudanar da rayuwarsu kamar na sauran mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here