Anyi kira ga Hukumar shiga da fice dasu kara sanya ido akan iyakokin qasashe da suka hade da Nijeriya

0

Anyi kira ga Hukumar shiga da fice dasu kara sanya ido akan iyakokin qasashe da suka hade da Nijeriya

Daga Zubairu T M Lawal Lafia

Masu ruwa da tsaki na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci a kara kaimi wajen dakile kwararowar bakin haure masamman yan gudun hijira daga kan iyakan qasashe, da suka hade da Nijeriya.

Masu fada ajin sun kara kira ga hukumomi tsaro na shiga da fice na kan iyakokin qasashe da su sanya ido sosai saboda yadda wasu yan gudun hijira daga wasu qasashen ke kwarara zuwa wasu sansanonin da ke wasu garuruwa a Nijeriya.

Hukumar bada tallafi ta Majalisar Dinkin Duniya ta koka game da yadda wasu yan gudun hijira ke barin tasu sansanin daga qasashen da suke su ketara zuwa wasu sansanonin daga wasu qasashe.

Tace ; wajibine a sanya ido saboda kowata sansanin yan gudun hijira da adadin mutanin da ake ajiyesu. Da zarar wasu sun shigo cikinsu to tsare tsaren da suke dashi na adadin abinchi ko ruwan ko kayan more rayuwar da aka ajiye yakanyi qaranci saboda zuwan baki.

Jami’an daga kungiyoyi na Majalisar Dinkin Duniya sun gabatar da wanan kudurince a babban taron ta da ta gabatar cikin wanan shekarar. Tace; wajibine Hukumar tsaro ta shega da ficen kan iyaka ta Nijeriya data zage dantse ta dauki matakin dakile dun wani xan ko yan gudun hijira da zasu riqa shigowa qasan nan ba tare da iziniba.

See also  KILA YAU A KAI ABDULMUMINI SHEHU SANI KOTU..

Shima a nasa jawabin Mista Brigitte Mukanga Eno wanda ya wakilce Mataimakin Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa ta Ofishin Hukumar bada abinchi ta Duniya a Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Tarayyar Afirika , ya yaba da wanan matakin da Masu ruwa da tsaki na Majalisar Dinkin Duniya suka dauka kan hana kwararuwar wasu yan gudun hijirar zuwa wasu qasashe da ba nasu ba.

Sanan ya bukaci da Manyam kungiyoyi masu fada aji dasu kara fadada taimakon da suke badawa domin taimakawa yan gudun hijira dake rayuwa cikin kunci a sansanoni.

Ya kuma roki da a kara kula da hakokinsu da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin su. Yace; bakowane yake fatan ya ganshi cikin wanan gurinba amma idan ta kama dole babu yadda Mutum zaiyi.

Yace; yadda yara qanana ke tafiyar da rayuwarsu a sansanin yan gudun hijira a kara fadada anyar taimako da za’arika koyar dasu Sana’a da zasu girma a kanta .

Shima da yake zantawa da manema labarai mai bada shawara ta masamman a ofishin bada agajin gaggawa Mista Abdulrahaman Balogun yace ya wajaba kan Gwamnatin qasan nan data tsaurara matakan tsaro akan iyakokin qasan nan saboda asan wasu irin jama’a ne me kaiwa da komowa zu qasan nan. Shima Farfesa Aderanti Adepoju yayi kira ga Hukumar bada tallafin abinchi ta Duniya data kara yawan abinchi da ake baiwa dalubai na sansanin gudun hijira da jama’an sansanin baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here