ANYI WA GIDAN SARKIN DAURA KAWANYA.

0

ANYI WA GIDAN SARKIN DAURA KAWANYA.
~~~Da saninmu aka yi “Sakataren Gwamnatin Katsina”
~~~”Mun bi umurnin gwamnatin jiha ne” Inji kakakin rundunar ‘yan sanda.
@ taskar labarai

Sakataren gwamnatin jihar Katsina Malam Mustafa Inuwa ya bayyana wa manema labarai cewa da sanin gwamnatin jiha jami’an tsaro suka killace fadar sarkin Daura.

Malam Mustafa Inuwa yace a tsari duk inda aka samu wannan cuta ana killace wajen haka yake a duniya don a gidan an killace don dauki awon duk wanda ke gidan don ayi masa binciken cutar ta Coronavirus.

Kakakin rundunar ‘yansanda ma ya kara jaddada wannan matsayin na cewa jami’an tsaro sun bi umurnin gwamnatin jiha ne suka killace gidan.

Yace ‘yan kwamitin dake yaki da wannan cuta wadanda suke aiki da jami’an tsaro sune suka bada shawarar. Wani da bai so a bayyana sunansa cikin ‘yan kwamitin ya bayyana cewa sarkin yana gaban kanshi wajen saba dokokin da aka dora na hana taruwar jama’a ciki har da bayar da kayan azumi.

Taskar Labarai ta gano a fadar an cigaba da hidimar tara mutane ana buda baki kamar yadda aka Saba. Kuma a ranar Alhamis ya nada matarsa giwar sarki a wani buki da aka yi cikin gidan kuma an tara mutane ‘yan kadan amma bidiyon dake yawo ya nuna an yi taron kafada da kafada.

See also  Atiku Yana Wata Muhimmiyar Ganawa Da Gwamnonin PDP Akan Fitar Da Gurbin Mataimaki

A kuma ranar juma’a aka yi wani taro inda ya rabar da kayan azumi ga mabukata inda har wata mata ta haihu a wajen turmutsutsi, ana jin jariran da ta haifa guda biyu suka shiga wani hali.

A ranar asabar hada kan jami’an suka mamaye gidan ba shiga ba fita kamar yadda wani daga cikin gidan ya tabbatar ma da Taskar Labarai.

A ranar lahadi jami’an yaki da Coronavirus sukaje fadar suka debi duk samful na wadanda aka killace a gidan. Majiyarmu ta tabbatar mana gidan zai kasance a cikin kawanya har sai sakamakon samful dinsu da aka diba ya dawo, wanda yana iya daukar kwanaki.
_______________________________________________
Taskar Labarai na a bisa www.taskarlabarai.com da kuma ‘yar uwarta ta Turanci a www.thelinksnews.com da duk shafukan yanar gizo.duk sako ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here