AREWA PROGRESSIVE YOUTH VANGUARD
AYI ADALCI A ZABEN SHUWAGABANNIN JAM’IYYAR APC.
Daga: Comrade Mukhtar Yahaya Alkatsinawy
Jam’iyyar APC ita ce Jam’iyya mai mulki wadda ta samu karbuwa ga al’umma musamman talakawa, sanadiyyar jagoranta Shugaba Muhammad Buhari da kuma hazikan dake cikinta.
Sai dai a jihar Katsina jihar shugaban kasa ana ta cece kuce akan Jagorancin Jam’iyyar kamar sauran jahohi an samu ra’ayoyin daban-daban.
Sai dai Alhamdulillah shugaban kwamitin shirya zaben kuma shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal mutum ne jajirtacce mai kokarin kamanta gaskiya kamar yadda shima gwamnan jihar Katsina ke bukata.
Sai dai wani jan hankali shi ne indai har ana son biyayya da nasara hadi da cigaba to ayi adalci ga wadanda ‘yan jam’iyya ke so hakan shi ne zai taimaki demokaradiyya a kasarmu dama jiharmu da ita kanta jam’iyyar APC.
Tabbas akwai kura-kurai wanda a fili suke kuma Ya kamata a duba su zan bada misali da guda daya zuwa biyu.
A Hedikwatar Jam’iyyar APC in kaje zaka ganta kamar kufai jam’iyya mai gwamna da anatoci da ‘yan Majalissunmu Na tarayya da na Jihohi da sauran manyan gwamnati hakan matsalace babba.
Sannan ‘yan kwamitin rumfuna an maidasu hoto sai lokacin zabe ake nemansu, hakika wannan matsaloline da ke cutar da demokaradiyya da ita kanta jam’iyyar APC.
Tabbas ina magana ne kan Jam’iyyar APC don ita ce ke mulki amma hakan ba zai hana ita ma PDP mu bibiyeta ba domin cigaba muke nema a jiharmu da arewacin Nijeriya to ta yaya zamu samu cigaba in bamu sanya adalci a cikin ayyukanmu ba?
Rashin yin adalci babbar matsalace don haka muke rokon ayi kokari a kamanta adalci, domin kasar nan baki daya Jihar Katsina ta sanya ma ido taga ya zata gudanar da zabenta Na Chiyomomin Jahohi tun da an san Katsina nan ne cibiyar siyasa kuma nan ne Jihar shugaban kasa sannan mai girma gwamnan Katsina da shi aka kafa wannan Jam’iyya kuma Dattijo ne mai Dattaku, Sannan akwai mutane masu Dattaku a cikin Jam’iyyar nan, don haka zamu sanya ido muga irin dattakun da za a nuna.
Amma ayi adalci don Allah.
Domin mutane suna sakaci wajen kamanta adalci a rayuwarsu wanda hakan kuskurene babba a matsayinmu na musulmi ko kirista mun man mahimmancin adalci a cikin addinanmu.
Sannan mun san irin masifar da ke biye da rashin adalci ya kamata tunda mu Musulmi ne mu kwatanta halin Annabin Rahama kuma Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W) wajen kamanta adalci, amma ba zamu saka ido muga ana yin rashin daidai ga al’ummar Arewa ba, koma wace Jiha ce mu kama baki muyi shiru hakan kuskure ne.
Koma wace Jam’iyya muka ga tayi kuskure ko tana neman tayi to muyi mata tirjiya a dinga barin mutane suna zabar Shuwagabannin su da kansu don samun maslaha da kwanciyar hankali da kuma cigaba a yankinmu na Arewa.
Naga zabukan baya tabbas Jiha r Katsina an yi kokari an kamanta adalci sosai to amma a nan muke bukatar muga ainahin adalcin.
.. muktar yahya .Alkatsinawiyyi shine shugaban kungiyar arewa progresive youth vanguard. Jami I, ne a kungiyar muryar talakka reshen jihar katsina
08066638362