BA BU TABBACIN CUTAR KORONAVIRUS A KATSINA….INJI BABBAN SAKATAREN LAFIYA .

0

BA BU TABBACIN CUTAR KORONAVIRUS A KATSINA….INJI BABBAN SAKATAREN LAFIYA .
Daga taskar labarai

A wata zantawa da manema labarai suka yi da Baban sakataren ma’aikatar Lafiya na jihar Katsina ya bayyana cewa, yawan samun kiraye-kiraye da suke kan wani da ake zargi yana dauke da cutar Caronovirus (Covid-19) a jihar Katsina ya sanya suka kira taron manema labarai domin sanar da mutane halin da ake ciki.

Sakataren ya bayyana cewa shi wanda ake zargin da kamuwa da cutar shi ya kawo kansa asibiti amma alamun da ya fadi ba alamun mura ba alamun mashako, ba kome, wata kila abinci ne ya ci gudawa ta kama shi. Amma saboda wannan tarihin da ya bada na cewa yazo daga Maleshiya, shi ne kawai aka ga cewa ya kamata a bincike shi a tabbatar da wannan abu ba zai zama wani abu ba. Wannan kuma umurni ne daga cibiyar kula davlafiya ta kasa wadda ta bayyana cewa duk wani bakomda ya dawo gida Nijeriya, in dai ya zo da wasu alamu na rashin lafiya to a bincike shi kuma tabbatar da baindauke da cutar.

See also  JAHAR KATSINA TA KAUCEWA ZAƁEN MUTUM BAYAN MUTUM

To saboda yawan kiraye-kiraye da muka samu daga wurare mabambanta shi ya sa muka ce bari mu kira wannan taro na manema labarai domin mu sanar da mutane kuma a kwantar dachanakalin al’umma a matakin cikin gida.

Amma zuwa gobe in muka samu sakamako zamu sake kiran taron ‘yan jarida domin sanar dasu halin da ake ciki, mun aika sample din jinisa Abuja da Legas domin a auna a tabbatar in an auna an tabbatar akwai zamu sanar in babu kuma zamu sanar, gobe in Allah ya kaimu zamu kira babban taron ‘yan jarida wanda kwamishinan lafiya zai masu bayani kan halin da ake ciki.

Ya bayyana cewa rubuce-rubucen manema labarai ne ya kara zafafa abun amma ba gaskiya bane, babu wani da aka tabbatar da cewa ya kamu da wannan cutar a jihar Katsina.
………………………………………………………………………
Jaridar taskar labarai da yar uwarta the links news. Jaridu ne dake bisa yanar gizo akan www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com suna kuma bisa sauran shafukan sada zumunta. 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here