BABBAR NASARA DAGA ALLAH

0

BABBAR NASARA DAGA ALLAH

Daga Datti Assalafiy

A yammacin jiya Laraba 26-6-2019 karnukan wutar jahannama annoba ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka yi zuga tare da kaddamar da mummunan harin ta’addanci a sansanin dakarun sojin Nigeria dake kauyen Goniri a jihar Yobe

Sai dai wannan harin bai yiwa ‘yan ta’addan yadda suka so ba, domin sojojin kundunbala sun mayar da mummunan martani ta sama da kasa, an musu ragaraga, sojojin sun hallaka adadi mai yawa daga cikin ‘yan ta’addan wanda har zuwa yanzu ba’a kai ga tantancewa ba

Sannan an kwato manyan makamai daga gurin ‘yan ta’addan, tare da lalata motocinsu na yaki a lokacin harin

See also  GENERAL FADAH COMMENDS BAYELSA GOVT FOR SUPPORTING NYSC 

Alhamdulillah wannan nasara daga Allah ne, jinjina gareku sojojin Nigeria dakarun Janar Buratai

Muna rokon Allah Ya taimaki sojojin Nigeria Ya kara musu cikakken nasara akan ‘yan ta’addan Boko Haram Amin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here