BAI KAMATA BA DUKAN MATA

0

BAI KAMATA BA DUKAN MATA …INJI IBN SINA

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar Hisba ta jihar Kano tace a cikin sati biyu da suka gabata ta na samun korafi da dama daga matan aure na cin zarafin da mazajensu ke yi ta hanyar lakadamusu dukan tsiya.

Babban kwamandan Hisbah na jihar Kano Muhammad Harun Sani Ibn Sina ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a yammacin Talata.

Ibn Sina ya ce galibin matan sun koka kan yadda mazajensu ke cin zarafinsu da tsakar rana, amma da zarar dare yayi sai kuma su fara lallabasu.

Ya ce mata amanace a wurinsu kuma abokanan zama ne da Allah ya tsara rayuwarsu tare.

“Irin dukan da aka kawo mana wata ma an lahanta mata idanu, wata kuma kafadarta, kana gani zaka ce cizo ne.

See also  'A SHIRYE NA KE NA AMSA KIRAN KOCIN NIGERIYA IDAN AN KIRA NI'---inji Mustapha Ibrahim

“Ko kadan wannan bai dace ba, kuma ina so na ja hankalin maza kan cewa a bi a hankali kada a ketare iyakar ubangiji.

“Mun sani ana cikin wani hali na wahala da kunci, Allah zai kawo mana mafita da yadda za a yi.

Haka zalika shehin malamin ya ja hankalin mata da suma su guji duk wani al’amari da ka iya harzuka mazan nasu.

Acewarsa matukar suka yi biyayya suka gujewa dukkanin abinda ba ya kan tsari to za su kaucewa wannan matsala.

Sannan Ibn Sina ya ce a addinance da hukumance wannan yaci karo da koyarwar addinin islama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here