BALA ABU MUSAWA NE ZABINMU
~~~Gamayyar Kungiyoyin Goyon Bayan APC na Shiyyar Daura.
Daga bishir mamman
@ katsina city news
Kungiyar wadanda suke da wakilci a kananan hukumomin yankin sanatan Daura, karkashin shugabancin Sani Abdurrahman da mataimakiyarsa Hadiza Mamman.
Suna goyon bayan Bala Abu Musawa a matsayin shi na jajirtacecen dan APC da bai taba wata jam’iyya ba da ya ja ragamar jam’iyyar a wannan zaben da za a gudanar 2 ga watan Oktoba Mai zuwa.
Sun bayyana shi a matsayin mai biyayya ga dokoki da ka’idojin jam’iyya kuma masoyin gwamna da shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaskiya.
Sun kara da cewa, tun da ake ba a taba jin shi yayi wa jam’iyyarsa zangon kasa ba. Yana kuma tare da mutanen sa daram na kananan hukumomin Musawa da Matazu.
Haka kuma kowa ya san shi wajen kamanta adalci da yin raba daidai a harkokin jam’iyya da zamantakewa.