BAMAI BAMAI SUN TASHI A FILIN JIRGIN SAMAN KATSINA

0

BAMAI BAMAI SUN TASHI A FILIN JIRGIN SAMAN KATSINA

Daga jaridar taskar labarai

Da misalin karfe uku na yammacin yau, laraba 12 ga yuni. wani jirgin saman yaki masu kai Hari ga yan taddan dazuzzukan zamfara da katsina ..yayi saukar gaggawa.a filin jirgin bayan ya tashi da misalin karfe daya na rana.
Yana sauka bama baman da yake dauke dasu sai suka fara fashewa. Wani bam din in yayi sama sai ya sauka bayan filin jirgin sannan ya fashi.
Mutanen da ke makwabtaka da filin jirgin sun ce fashewar ta kai hamsin.
Wakilan mu da suka isa filin jirgin uku da rabi na yamma a lokacin fashewar bata tsaya ba. Sojoji sun killace filin jirgin ba shiga..sai dai fitowa.
Wakilan mu sunga waje biyu wajen filin jirgin da bam din ya fado ya fashe.
Har zuwa rubuta labarin nan..ma aikatan kashe gabara na kokarin kashe wutar.mun samu tabbacin ba wani asarar rai .ba kuma wata kadarar filin jirgin mai tsada da shafu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here