BARAYIN MUTANE SUN KAI HARI GARIN BATSARI
Daga Taskar labarai
Barayin da kan saci mutane don neman kudin fansa sun kai hari garin batsari jiya da dare ,
Shaidu sun fadawa taskar labarai cewa maharan sunje garin da misalin karfe goma sha daya na daren jiya.laraba inda suka je wata unguwa kusa da bakin garin .maharan sun harbe wani mutum ya mutu nan take .sun kuma tafi da wata mata mai ciki da danta da wani matashi wanda ke sana ar sayar da ruwa a kura. Da kuma wani tsoho wanda daga baya suka sako shi
Maharan sun tafi da mutane biyar a cikin daren
Wani jami in karamar hukumar ta batsari ya fada wa taskar labarai cewa a cikin daren ya kira yan sanda .amma abin takaici basu da mota domin an kona motarsu kwanakin baya
Jami in yace sai suka nemi taimakon sojoji.wanda jin zuwan sojan ya sa barayin suka bar garin cikin sauri.