Bashir Nura Alkali ya zama babban sakataren Ma’aikatar Harkokin Jinƙai

0

Bashir Nura Alkali ya zama babban sakataren Ma’aikatar Harkokin Jinƙai

Bashir Nura Alkali ya kama aiki a matsayin sabon Sakataren Dindindin (Permanent Secretary) na Ma’aikatar Harkokin Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa ta Tarayya.

A wajen bikin karɓar aikin a harabar ma’aikatar, sabon Sakataren Dindindin ɗin ya bayyana jin daɗin sa ga Ministar ma’aikatar, Hajiya Sadiya Umar Farouq, da daraktoci da dukkan ma’aikatan ma’aikatar, saboda kyakkyawar karɓar da aka yi masa tare da shan alwashin bada dukkan gudunmawar da ake buƙata wajen cimma ƙudirorin ma’aikatar.

Alkali ya kuma buƙaci haɗin kan dukkan ma’aikatan wajen takalar ɗimbin ƙalubalen da ke gaban ma’aikatar.

A jawabin sa, darakta mai kula da Ofishin Sakataren Dindindin ɗin, Grema Ali Alhaji, a madadin Minista Sadiya Umar Farouq da kuma daukacin dukkan ma’aikatan ma’aikatar, ya yi wa babban sakataren marhabin da zuwa.

A jawabin sa na miƙa sandar kama aiki a gare shi, Grema ya yi la’akari da cewa an kafa ma’aikatar ne ta hanyar furucin da shigaban ƙasa ya yi a ranar 21 ga Agusta, 2019 kuma ɗaya daga cikin ayyukan da aka ɗora mata shi ne tattaro tare da kula da ayyukan jinƙai da taimakon jama’a a Nijeriya. Ya ƙara da cewa tun daga lokacin da aka kafa ma’aikatar, Minista Sadiya tare da goyon bayan ma’aikatan sun yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da cewa an saisaita ma’aikatar a kan turbar gudanar da ayyukan da aka ɗora mata kamar yadda ya kamata.

See also  KA IDOJIN SAKA LABARAI A KATSINA CITY NEWS

Ya bayyana cewa wasu daga cikin ƙalubalen da ma’aikatar ta fuskanta da farko sun haɗa da batun kafuwar ta, harkokin gudanarwa da batun kuɗi, kuma ya zuwa yanzu an warware yawancin waɗannan matsalolin ko kuma ana kan warware su.

Ya ce, “Bin tsarin haɗa komai waje ɗaya kuma a zahiri ga kowa wajen gudanar da duk wani aiki ya samu kulawa daga jawadawalin tsarin gudanarwa da ta hanyar daidaita shi da jerin sunaye da ayyukan ma’aikata wanda ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na Tarayya.

Mataimakiyar Darakta a sashen Yaɗa Labarai na ma’aikatar, Madam Rhoda Ishaku, ta ruwaito Grema ya na tabbatar wa da sabon babban sakataren cewa zai samu dukkan tagomashi da tallafi daga kowane ma’aikaci wajen gudanar da aikin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here