Bello matawalle ya bada tallafin miliyan biyu ga wadanda suka sami haddari a zamfara

0

Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnan jihar zamfara, Hon Bello matawallen maradun yayi alkawalin baiwa wadanda suka sami hadarin Mota a ranar larabar da ta gabata gudummawar Naira miliyan 2 ga iyalan
kowanne mamacin wanda ke da mata, sai Naira miliyan 1.5 ga iyalan wadanda ba su da aure a cikin su.

Hakan ya fitone cikin wata takarda wadda ke dauke da sa hannun, Daratta janar na yada labarai na Fadar Gwamnatin jihar , Alh Yusuf Idris Gusau,
ya Kara da cewa zai sanya dangin kowane daga cikin wadanda abin ya shafa a kan alawus na Naira dubu 50 kowane , ya ce
za su ci gaba da kasancewa a cikin jerin albashin jihar har zuwa karshen lokacin da ya ke gwamnan jihar.

Ya Kara da cewa gwamnatinsa za ta gabatar da amfani da na’ura na auna saurin gudu a kan manyan tituna da kuma auna nauyi a kan manyan motoci da kuma gwajin magunguna a kan direbobi domin kaucewa tukin ganganci da rikon sakainar kashi wanda galibi kan jawo rasa rayukan mutane.

See also  NITDA trains over 800 children on STEM

Matawalle ya ce daukan matakan sun zama dole saboda direbobi da danginsu ba za su kara tunanin za su samu sauki ba idan direbobin suka kashe wani, domin a cewarsa rayukan ‘yan jihar sun fi kowane abu muhimmanci.

Mnatawalle wanda ya nuna alhininsa kan mutuwar mutane 15 da suka rasa rayukansu sakamakon tukin ganganci da wani direban babbar mota ya yi a ranar Larabar da ta gabata a kan hanyar Gusau zuwa Funtua.

Gwamnan ya jagoranci mambobin majalisar zartarwarsa da kuma Shugabannin kungiyar BUA zuwa ziyarar ta’aziyya ga Sarkin katsinan Gusau Alhaji Ibrahim Bello , kan mutuwar mutane 15 daga masarautar .

Idan ba’a mantaba a ranar larabar da ta gabatane aka sami mummunar hadarin mota wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 15 da suka rasa rayukansu sakamakon tukin ganganci da wani direban babbar mota ya yi a ranar .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here