Mu’azu Hassan
@ Katsina City News
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mayakan Ansaru na bangaren Boko Haram sun dawo dajin da ke garin Danmusa da ke garin Katsina.
Binciken da jaridunmu suka yi sun gano lallai mayakan kungiyar Ansaru sun je wani gari mai suna Bicci da ke kusa da Mara a Karamar Hukumar Danmusa a ranar 16 ga Yuli, 2022.
Ganau sun tabbatar wa da jaridunmu cewa mayakan sun je garin ne a kan babura suka nemi gidan Maigari, kuma suka zauna da shi da isar masa da sakonsu.
Ganau sun ce, mayakan sun rika zama can cikin daji ne, amma suna aiko ’yan aike su yi masa sayayya abun bukata da kuma tattaunawa da mutanen gari.
Ganau sun ce sun rika hira da mutanen kauyukan yankin, amma ba wata tsangama ko takurawa.
Ganau sun ce daga baya an bar ganin su kwata-kwata, hatta makiyaya da ke hangen inda suka yi sansani sun bar ganin su.
Mayakan da ke da alaka da Boko Haram suna shawagi a dazuzzukan Sabuwa, Faskari, Kankara da Dandume, yanzu ne suka fara shigowa har Safana da Danmusa.
Bincikenmu ya tabbatar duk dazuzzukan da ke Jihar Katsina ba su da sansani har yanzu.
Mayakan masu alaka da Boko Haram in za su kafa sansani sukan nemi hadin kan barayin dajin da ke yankin.
Bincikenmu ya gano har yanzu ba a samu wannan fahimtar juna din ba. sai dai alaka ta hadin kai ta dukkaninsu suna fada da gwamnati da makamai ne.
Wani dan bindiga da ya yi ikirarin tuba, ya tabbatar wa da jaridunmu cewa, barayin dazuzzukan Katsina suna tsoron ba mayaka masu alaka da Boko Haram mafaka don kar su kore su, su mamaye wurin.
Wani masanin yadda mayakan ke tafiyar da al’muransu ya ce in ka ga suna yawan zuwa waje akwai abin da suke nufi, ko akwai mummunan shirin da suke wa wajen.
Ko a kwanakin baya wasu wasiku sun rika yawo a Katsina wadanda ake zargin wasu bata-gari ne suka aika da barazanar kai hari wani wuri.
Jaridunmu sun samu kwafi daya na wasikar wadda wani wai shi Amir ya sanya wa hannu.
Bincikenmu ya gano jami’an tsaro, musamman na farin kaya suna bakin kokarinsu, inda suka kama ‘Bandit’ da suka dawo gari suka zauna, wanda ake zargin suna sa ido ne don shirya wata makarkashiya.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245