BUHARI YANA KYAUTA NI SHAIDA NE

0

BUHARI YANA KYAUTA .NI SHAIDA NE …
Daga dakta Aliyu tilde

(Tsakuren dina da wani ya ce Buhari ya ba wani masoyinsa dubu hamsin kacal bayan ya gayyace shi villa)

Wata rana, a 2002, mun dau jirgi da Buhari zuwa Jos don wata lacca a UNIJOS. Da muka gama muka dawo Haipang Airport, Jos, muna jiran a kammala kimtsa jirgi sai ya ce in miko mar jakar hannunsa. Sai ya bude a tsanake ya ciro bandir din N200 na N20,000 ya ba ni na mika wa ma’aikatan airport din da suka zo gaishe shi. Na mika musu, sai na juya, na ji kwalla sun sabko mun. A zuciyata na ce, “Allah sarki da yana da dukiya mai yawa da ya ba su da yawa—ashe yana kyauta.”

Ita kyauta zuciyar da ta ba da ita ake duba wa ba yawanta ba. Almutanabbi ya ce, “Kad’an daga masoyi, mai yawa ne.”

Ina tunawa mun hadu da shi a Makka ya zo umrah ni kuma na fito Riyadh a 2003. Da jama’a suka watse sai ya dauko wani tarin $100 ya ce, “Ga wannan Dr.” Sai na ce masa, “Ranka ya dade ka fi ni bukatarsu saboda jama’a da kake fama da su a cikin siyasa.” Sai ya ce, “Dr. halinka ke nan. Amma dole ko daya ce ka karba.” Na mika hannu na karba na ce na gode. $100 din nan ta faranta min rai saboda zuciyar da ta bani ita cikin annashuwa da fara’a.

Ina tuna labarin da wani aminina, former VC na UDUS, ya ba ni. A shekarar 1975, yana dalibi, ya je ya ofishin Buhari yana Gomna a Maiduguri don ya nema wa MSS gudunmawa na yin Annual National Conference. Buhari da ya ji daga Zariya suke kuma suka gaya masa abinda ya kawo su, sai ya ce a kai su gidansa su ci abinci sannan a dawo da su.

Da suka dawo sai ya ce musu su yi hakuri babu irin wannan kudin a kason kudin gomnati—watau budget. Amma sai ya dauko N200 tasa ya ce ga gudunmawarsa ta kashin kansa.

Ina ga mutane da yawa da suka bi Buhari ba su fahimci yadda yake kallon abubuwa ba. Mutum ne mai tsananin fulaku da kara da kamun kai da yin abu daidai karfinsa. Wannan hali nasa har abada yana burge ni kuma abin koyi ne. Bature ma zai ce, to a fault, don har ta kai Buhari ba ya tsawatawa na kasa da shi saboda kara. Da ake ta kuka da na kusa da shi wadanda suka jagoranci CPC, sai ya ce toh ya zai yi da su tunda sune a jinkinsa?

A daya bangaren kuma ba zai ce a baka mukami ko kwangila ba saboda abotarku. Sai dai idan an ba ka a karkashinsa—koda kuwa danginsa ne kai—ba zai ce komi ba. Wannan abinda wadanda suka yi masa hidima a siyasar 2015 ba su gane ba ke nan. Ka masa bisa akida kawai amma ba don ya biya ka ba. Ya ce gyaran mulkin da zai yi shi ne sakayyar duk wanda suka taimaka masa a bisa akida. Da na ji wannan bayani nasa a rediyo sai na yi ihu na ce, “Aha Oga”. Da Mbaka ya je wajen wasu kasa da Buhari ne da ya samu biyan bukata fiye da tinkarar Buhari.

Akwai wani aminina a Bauchi wanda ya fi kowa yi wa Buhari hidima idan ya zo Bauchi tun 2002. Abinda ya hada su shi ne abokin nawa ya gyara wa Buhari gidansa na Daura a 1995 ta yadda Buhari ya ji dadi sosai. Da aka kafa PTF har an yi nisa da ayyuka sai Buhari tambayi Salihijo ina abokinsa da ya gyara masa gidan Daura kuma wane aiki aka ba shi ya yi? Sai Salihijo ya ce ai ba a ba shi kwangila ba. Sai Buhari ya ce, “Ayya.” Bai ce komi ba bayan nan. A nan Salihijo ya gane yakamata ya yi wani abu.

A yanzu ma duk da kaunar da ke tsakninsa da Buhari, ba a ba shi mukami ko kwangila ko ta sisi ba a karkashin wannan gwamnatin. Kuma duk da mawuyacin halin da abokin nawa yake ciki bai taba kokawa kan Buhari ba ko mukarrabansa wadanda duk sun san shi. Akwai manyan ministoci ma da suka san shi da Buhari amma ko board member ko yar kwangila ba su jefe shi da ita ba. Amma tunda a bisa akida yake tare da Buhari kuma ya san halinsa, sam bai taba cewa uffan ba.

Ni ma a 1997 na taba rugawa wurinsa don ya sa baki a ba ni wata kwangila da na kwallafa raina a kanta kuma an mun alkawari amma kawai sai ya ce, “Dr. Allah sa dai ba a yi latti ba ko?” Af. A nan ya bar maganar. Na rasa kwangilar. A nan na gane abin da wani dan’uwansa ya taba ce mun ai ba ya sa baki don a ba mutum wani abu, lokacin yaron ya same ni a garden din Buhari a Kaduna ya ce in taimaka masa ya shiga NDA, ni kuwa na ce masa, “Kai da kake da General?”

See also  Wataƙila nan da shekara uku ku fara hawa tasi mai tashi sama

Bayan an raba mukamai a 2015, sai a 2016 shugabannin Buhari Support Organization na wasu jihohi suka samu Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir suka ce masa su fa ba su gane ba. An je yaki da su amma an raba mukamai sun ji shiru. Suna so su ga Buhari. Sai Babachir ya ce musu a gaskiya Buhari ba haka yake ba kuma ba abinda zai musu. Sai dai wadanda cikinsu suka san ministoci su je wajensu su yi baran wani abu. Da guda daga cikinsu muka yi wannan maganar.

Kuma na sha jin mutane da yawa suna ce Buhari yana da keta da riko. Gaskiya da wuya in yarda. Karamin misali shi ne ni. Na rabu da shi a 2010. Tun lokacin bai sake ganina ba kuma na goya wa Ribadu baya bisa imanin zai fi dacewa da mulkin mutanen Nijeriya da sauran dailai irin sanyi da tsananin kara irin ta Buhari da har ya kasa daukan mataki kan lamurran da suka addabi CPC. Na rubuta haka karara a jarida da yanar gizo a 2011. Amma duk wannan—wanda wasu suka ga cin mutuncin Buhari ne—bai hana har gobe Buhari ya kirga ni cikin mutanensa biyar mafiya girma a Bauchi ba. Da yana da riko, ni kam da na sha dauri sai igiya ta saura. Da ko batuna ba zai yi ba akalla.

Amma don kyauta kam da kara, Buhari yana da su. Kuma abu biyu game da shi wanda na fi so ke nan. K’in sa bakinsa kai tsaye a kwangila da ba da mukami kuwa, a ganinsa, kare mutuncinsa (integrity) ne wanda tsohon halinsa ne tuntuni. Yana da wahala cikakken Bafulatani ya yi roko ko da wajen danginsa ne kuwa. Fulani na cewa ka tambaya an ba ka yaya kunyar balle ka tambaya a hanaka? Da kuma gudun zargi. Ko list na mukamai a karkashinsa a matsayin shugaban kasa sai dai su ‘cabal’ ko komiti su tsara amma ba shi ba. Idan mutum bai sani ba sai ya dauka ya mance da shi ne. Wallahi sam. Ya san duk wanda ya yi mar, hairan ko sharran. Kuma ba wai hassada ba ce ko keta ko mugunta ce da shi ba. Ko daya Buhari ba yi da wannan. Idan ka fahimce shi shi ke nan.

Wajen da kawai na bambanta da shi shi ne kara a guna tana da iyaka musamman ga mai mulki kamar yadda na rubuta a nasihata gare shi a farkon mulkinsa. Wasu yan’nijeriyan wallahi sai da murtuke fuska, da muzurai, da tsawa, da barazana, da takewa da takalmin karfe kafin mulki ya yi karko. Idan ba haka ba, kan ka ce kwabo yan’iska sun mamaye ka sun bata maka mulki. Ina bakin cikin cewa wannan shi ne ya faru a wannan zubin mulkin nasa da bai yi sa’ar makusata ba.

So wanda Buhari ya ba shi N50,000 yana shugaban kasa kar ya dauka rowa ne. Da kudin ya fi haka ma, da irina sun tuhumce shi. Ya yi murna ya kira shi villa—Wayyo villa!—sun gaisa har ya masa kyauta saboda kauna da mutunci. Kar ya duba yawan kudin.

Akwai wani komishina a Bauchi, gyauron Buharin 1975 da 1984, shi ma yana kyauta amma irin ta Buhari—daidai ruwa daidai gari. Sai yan’siyasa su rika cewa ba shi da kyauta… Gane mani hanya…In ka zo ofis dinsa sai ya kawo maka zancen ilimi ya ce ko ka zo a taimaka wajen ilimin yaranka ne. Da ka ce maula ta kawo ka ko neman kwangila sai ya ba ka hakuri. In ka ci sa’a ya sa hannu a aljihu ya debo daga canjinsa ya ba ka. To kudin jama’a zai dauka ya ba ka? Amma shi wannan komishinan zafi gare shi ba kamar maigidansa ba. Kar ka yadda ya kama ka da laifi na ganganci. Wallahi za ka fi aya zafi. Tabdi jam. Bone! ?

Ita shaidar gaskiya ta zama dole a fade ta a kowane hali.

Dr. Aliyu U. Tilde
2 Mayu 2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here