Buhari Zai Yi Kwanaki Hudu A London Don Ganin Likita
A yau Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa birnin London domin duba lafiyarsa.
Wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar ta ce Shugaba Buhari zai shafe kwaki hudu likitocinsa suna duba shi.
A jiya Litinin ne aka fitar da sanarwar da daddare, kwana guda gabanin tafiyar shugaban zuwa London.
Malam Garba Shehu ya ce ko a makon da ya gabata ma Shugaba Buhari ya ga likitansa, lokacin da jirginsa ya yi ratse a kan hanyarsa ta komawa Najeriya bayan kammala ziyarar aiki a Amurka.
A cewar Kakakin na shugaban kasa ya ce a lokacin ne, likitan ya ce akwai bukatar sake duba lafiyarsa, inda kuma shugaban ya amince da yin hakan.